Nijeriya

Amurka Ta Tabbatar Da Aika Da Sojoji Zuwa Najeriya

Amurka Ta Aika Da Sojoji Zuwa Najeriya

Amurka ta tabbatar a hukumance da tura wasu tsirarun jami’an soji zuwa Najeriya a wani bangare na inganta hadin gwiwar tsaro da hukumomin Najeriya, musamman a kokarin yaki da ta’addanci.

A cewar cibiyar rundunar sojin Amurka ta Afirka, sojojin da aka tura za su ba da tallafi na musamman kamar musayar bayanan sirri da daidaita ayyuka, amma aikin bai kunshi zuwa filin daga kai tsaye ba.

Sanarwar ce amincewa ta farko a hukumance ga sojojin Amurka a Najeriya tun bayan harin da jiragen yakin Amurka suka kai kan masu tsattsauran ra’ayi a karshen shekarar 2025. Sai dai a sanarwar ba a bayyana takamaiman adadin sojojin na Amurka ba da kuma wuraren da za a jibge su.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button