Afirka

Birtaniya ta sanyawa kwamandojin RSF na Sudan takunkumi

Birtaniya ta kakaba wa kwamandojin RSF na Sudan takunkumi

Birtaniya ta sanyawa manyan kwamandojin rundunar Rapid Support Forces ta Sudan takunkumi a ranar Juma’a bisa zarginsu da alaka da kashe-kashen jama’a da cin zarafi ta hanyar lalata da kuma kai hare-hare da gangan kan fararen hula a kasar ta Sudan.

Abdul Rahim Hamdan Dagalo mataimakin shugaban RSF kuma dan uwa ga kwamandan RSF Mohamed Hamdan Dagalo da aka fi sani da Hemedti da kuma wasu kwamandoji uku da ake zargi da hannu a wadannan laifuka a yanzu haka na fuskantar dokar hana kadarori da kuma hana tafiye-tafiye.

Yvette Cooper
Yvette Cooper – Ministar Harkokin Waje na Birtaniya

Ministan harkokin wajen kasar Birtaniya Yvette Cooper ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa cewa, ta’asar da ake tafkawa a kasar Sudan na da matukar ban tsoro. “Takunkumin da aka kakabawa kwamandojin RSF a yau sako ne ga wadanda ke da hannu a zubar da jinin al’umma.”

Gwamnatin Birtaniya ta kuma yi alkawarin kara kudi har fan miliyan 21 don samar da abinci da matsugunai da kayayyakin kiwon lafiya domin samar da kariya ga mata da kananan yara a wasu yankunan da ke da wahalar zuwa, in ji sanarwar.

Matakin na zuwa ne bayan da Amurka da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar da kuma Saudiyya a farkon watan Nuwamba suka gabatar da wani shiri na tsagaita bude wuta na tsawon watanni uku sannan kuma a yi shawarwarin tabbatar da zaman lafiya. Rundunar ta RSF ta mayar da martani da cewa ta amince da shirin, amma jim kadan ta kai hari sansanin sojojin da jirage marasa matuka.

Miliyoyin mutane ne suka rasa muhallansu sakamakon wannan mummunar yakin, wanda ya barke a watan Afrilun shekarar 2023 tsakanin sojojin Sudan da RSF.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button