Nijeriya

Borno: Za a rufe sansanin ‘yan gudun hijira na Muna

Borno za ta rufe sansanin 'yan gudun hijira na Muna nan da makonni 2

Fadeelah Abdulmalik

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana cewa za a rufe sansanin ‘yan gudun hijira na Muna nan da makonni biyu masu zuwa.

Gwamna Zulum ya bayyana haka ne a wata ziyarar da ya kai sansanin.

Muna na daya daga cikin manyan sansanonin da ake tsugunar da ‘yan gudun hijira a daidai lokacin da ake fama da matsalar tallafin jin kai a jihar; duk da haka, kashi 75% na mazaunanta an sake mayar dasu matsugunnasu.

A wa’adin mulkinsa na farko, Gwamna Zulum ya yi alkawarin rufe dukkanin sansanonin da ke cikin Maiduguri da kewaye, wannan burin da ya cimma ya kai ga rufe sama da sansanoni goma sha biyu.

A yayin ziyarar gwamnan ya yi alkawarin tallafa musu da inganta rayuwarsu.

Sansanin Muna yana da mutane kusan 10,000 da suka rasa matsugunansu.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button