Idan Amurka ta kai hari, Iran za ta rama kan Isra’ila da sansanonin sojin Amurka
Idan Amurka ta kai hari, Iran za ta rama kan Isra'ila

A cewar jaridar The New York Times, har yanzu Donald Trump bai yanke shawara ta karshe ba, amma yana matukar duba yiwuwar amincewa da kai hari a matsayin martani ga yunkurin gwamnatin Iran na murkushe zanga-zangar.
Firaministan Isra’ila Netanyahu da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio sun tattauna kan yuwuwar shigar Amurka cikin kasar Iran. Kuma sun gabatar wa shugaba Trump zabi daban-daban, ciki har da kai hare-hare kan wuraren da ba na soji ba a Tehran.
Iran ta ce idan Amurka ta kai mata hari, za ta lalata dukkan sansanonin sojin Isra’ila da na Amurka a yankin.
Pakistan ta ce ba ta goyon bayan duk wani sauyin gwamnati a Iran, kuma tana goyon bayan al’ummar Iran kan duk wani mai tsoma baki daga kasashen waje.
Kakakin majalisar dokokin Iran Ghalibaf ya jaddada gargadin cewa idan Amurka ta kai hari kan Iran, sansanonin Amurka a yankin da kuma Isra’ila za su zama halaltacciyar guraren da Iran za ta kai harin ramuwar gayya.




