Mutane 33 sun mutu, wasu 33 suka jikkata a hadurra wutar lantarki a wata uku a Nijeriya
Mutane 33 sun mutu, wasu 33 suka jikkata a hadurra wutar lantarki a Nijeriya

Hukumar da ke rarraba wutar lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana cewa mutane 33 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 33 kuma suka jikkata a hadurruka masu alaƙa da wutar lantarki a faɗin ƙasar.
A cewar rahoton da hukumar ta fitar na wata ukun karshe na shekarar 2025, an samu jimillar hadurra 57 da suka shafi wutar lantarki.
Hadurran sun bazu a yankuna da dama da hukumar ke gudanar da ayyukan rarraba wutar lantarki, kana an fi samun hadurran a yankin Ikeja na jihar Lagos da kano a cewar rahoton hukumar
Ayyuka marasa aminci da yanayi masu haɗari su suka fi haifar da mafi yawan raunuka da ma’aikata suka ji da kuma mafi yawan mace-mace, yayin da gobarar waya ta zama ɗaya daga cikin hadurra mafi muni da aka samu wanda ya kai ga mutuwar mutane 10 da kuma wasu da suka jikkata har mutum bakwai a tsakanin wata ukun karshe na 2025.




