Volume
Offline Radio
Social
Networks
Shawara ta ga Ganduje shine ya koma Makarantar allo. - Ɗan Sarauniya
12/08/2021 12:31 in Siyasa

 

Aliyu Samba

 

Tsohon Kwamishina ayyuka na jihar Kano, kuma ɗan takarar Gwamnan jihar Kano Engr Muaz Magaji wanda aka fi sani da ''Ɗan Sarauniya'' ya ce Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na da buƙatar komawa makarantar allo.

 

Tsohon kwamishinan ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafin da na facebook a safiyar yau Laraba.

 

''Shawara ta ga mai girma Ganduje ba karatu a Havard ne kake da bukata ba, digirinka da PhD daga ABU da jami'ar Ibadan sun wadatar dakai, abin da kake bukata shine abin da ka rasa, Makarantar Allo.'' Inji Magaji.

Ya Kara da cewa, don fahimtar mataki da matsayin iyali a mulki da gudanar da amanar jama'a, fahimtar daftarin aiki da da'a wajen tafiyar da dukiyar al'umma, fahimtar nauyi da da'a wajen nada mataimaka masu nagarta da rikon amana, ka nemi ƙarin sani game da tsarin shugabancin Umar (RA), ba ka buƙatar ilimin Havard dan ka jagorance mu yadda aya kamata. 

 

Muaz Magaji ya taba samun Kujerar Kwamishinan ayyuka a gwamnatin Ganduje a shekara ta 2019, saidai a ranar 17 ga watan Afrilu, 2020 lokacin mutuwar Abba kyari, Muaz yayi wani rubutu akan shafin da na facebook wanda yayi sanadiyar sauke shi daga wannan kujera ta kwamishina a kano.

 

Daga baya Gwamnan ya kuma bashi Shugaban ayyukan isar da bututun mai na NNPC-AKK da kwamitin masana'antu na jihar Kano. 

 

Jarida Radio

8/12/2021

 

 

 

COMMENTS
Comment sent successfully!