Volume
Offline Radio
Social
Networks
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai Ziyarci jihar Lagos domin Bukin Kaddamar da Littafi
12/09/2021 07:56 in Najeriya

 

Daga Ahmad Kabo Idris

 

Rahotanni na nunar da cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai isa jihar Lagos a gobe Alhamis domin halastar taron bukin kaddamar da Littafi, mai taken “Rawar da na Taka” akan tarihin tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na riko Bisi Akande.

 

Ta cikin wata sanarwa da hadimi na musamman ga Bola Tinubu ya fitar, tace taron zai gudana ne a Otel din Eko Hotels and Suites, dake Victoria Island a birnin Ikko.

 

Sanarwar ta raiwaito Shugaba Buhari a matsayin Baban Bako na musamman yayin taron, sai gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu a matsayin mai masaukin baki, yayin da Jigo a jam’iyyar APC Bola Tinubu a matsayin Babban Bako.

 

Da yake bayyana ra’ayinsa akan Littafin da za'a kaddamar, Masanin Adabin Turanci da ya lashe kyautar Nobel Wole Soyinka, ya baiyyana tarihin da aka rubuta cikin littafin a matsayin babbar kyauta ga Kasa wanda da al’umma zata amfana a lokacin da ake ciki.

 

Akande ya kasance guda daga cikin ‘yan siyasa da sojoji suka kama bayan rushewar jamhuriya ta biyu a 1983. Sai dai ya shaki iskar ‘yanci a 1985 tare da alkawarin raba gari da harkokin siyasar kasa tin daga lokacin.

Jarida Radio

09/12/2021

#buharitravels #legos #booklaunching

COMMENTS
Comment sent successfully!