Volume
Offline Radio
Social
Networks
Gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar da sabuwar Jarabawar Gwaji ga Malaman Makaranta Dubu 35
12/09/2021 07:58 in Ilimi

Daga Ahmad Kabo Idris.

 

Gwanatin jihar Kaduna ta fara gabatar da sabuwar jarabawar gwaji ga malaman makarantar Firamari a wani mataki na tabbatar da ingantaccen Ilimi da koyarwa a makarantun dake fadin jihar.

 

Kimanin shekaru hudu da suka gabata, gwamnatin jihar ta gabatar da makamancin wannan jarabawar gwaji, wadda ta sabbaba korar malaman makarantun su dubu 22 da basu da kwarewar da ta dace.

 

A baya dai Matakin ya tunzura kungiyar Malaman makaranta ta Kasa da na Kwadago NLC yin Allah wadai da gwamnati, tare da gabatar da zanga-zangar lumana.

 

Duk da kurar da hakan ta haifar, gwamnatin jihar ta dauki sabbin malaman makaranta Dubu 25 domin cike gibin da aka samu.

 

Rahotanni sun nunar da cewa ana tsamannin malaman makarantar zasu amsa tambayoyi 10 daga kowanne darasi na Turani, da Lissafi da Ilimin zamantakewa da kuma Kimiyya.

Jarida Radio

08/12/2021

#schoolteachers #competancytest #kaduna

COMMENTS
Comment sent successfully!