Volume
Offline Radio
Social
Networks
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka birnin Lagos
12/09/2021 12:31 in Najeriya

Ahmad Kabo Idris

Da sanyin safiyar Yau ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tare da tawwagarsa suka sauka a filin tashi da saukar Jiragen sama na Murtala Muhammed.

 

Shugaban Kasar ya samu tarba ta musamma a filin jirgin saman daga Gwamnan jihar Lagos Babajide Sanwo-Olu da sauran mukarraban gwamnatinsa.

 

Yayin ziyarar, anan tsammanin Shugaban Buhari zai kaddamar da bude sabbin Jiragen Ruwan Sojoji da Jirage masu saukar Ungulu, yayin da kuma zai halarci bukin kaddamar da Littafin tsohon shugaban Jam’iyyar APC Bisi Akande.

 

A nata bangaren hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Lagos (LASTMA) ta cikin wata sanarwa da ta fitar, ta shawarci matuka ababen hawa akan hanyoyin da ya kamata suyi amfani dasu yayin shige da ficen su.

 

Sanarwar ta kara da cewa, za’a rufe titinan da suka hadar da na Ahmadu Bello, da mahadar Adeola Odeku zuwa titin Adetokunbo Ademola, da kuma shatale-talen Eko Hotels, inda matafi zasu iya amfanin da hanyar Adeola Odeku da Akin Adesola.

Jarida Radio

08/12/2021

#buharitravels #legos #nigeria

COMMENTS
Comment sent successfully!