Volume
Offline Radio
Social
Networks
'Yan bindiga sun kashe mutane 51 tare da kona gidaje a jihar Neja da Filato
01/13/2022 11:00 in Tsaro

Aliyu Samba

A safiyar ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a wasu kauyuka uku a jihohin Neja da Filato, inda suka kashe mazauna garin 51 kafin su tsere daga ƙauyukan.

An gano gawarwakin mutane 34 da aka kashe a yankin Nakuna da Wurukuchi na Neja a cikin daji da gonaki.

An ruwaito cewa 14 daga cikinsu ‘yan gida biyu ne, ma'ana yaya ne daga gidajen biyu a garin. 

A ranar talata din kuma wasu ‘yan bindigar sun kashe Mutane 17 a Ancha da ke karamar hukumar Bassa ta jihar Filato sannan suka kona gidaje da dama.

Hare-haren sun faru ne jim kadan kafin bayyanar da cewa an yi garkuwa da ‘yan kasuwa da dama a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna.

Kwamishinan ‘yan sanda Monday Kuryas da kwamandan rundunar tsaro ta Operation Safe Haven Maj.-Gen. I. S. Ali ba su yi jayayya da alkaluman ba.

 

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane a fadin kasar nan.

 

Shi ma shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya nuna damuwarsa kan kalubalen tsaro da ke kara ta’azzara inda ya ce ‘yan Najeriya na bukatar daukar mataki ne ba uzuri ba.

 

Hare-haren na Nakuna da Wurukuchi a safiyar ranar Talata an ce ramuwar gayya ce da ‘yan bindigar suka yi sakamakon a makon jiya ‘yan banga da mafarauta sun kashe abokan aikinsu da dama.

 

An ce ‘yan bindigar sun kama tare da kashe uku daga cikin mafarautan a daya daga cikin kauyuka biyun.

 

Jarida Radio ta samu labarin cewa mazauna garin 10 da aka kashe a Nakuna ‘yan gida daya ne yayin da wasu hudu suka fito daga wani gida a Wurukuchi.

 

Ba su yi kasa a gwiwa ba bayan kashe-kashen, ‘yan bindigar sun ci gaba da kona gidaje da rumbunan abinci a Nakuna.

 

Kwamishinan ‘yan sanda Kuryas, wanda ya tabbatar da kisan, ya ce an tura ‘yan sanda zuwa yankunan.

 

Jarida Radio ta tattaro cewa a garin Ancha dake jihar Filato yan bindigar sun kashe mazauna garin 17 tare da kona gidaje da dama.

 

Jami’in yada labarai na Operation Safe Haven Ishaku Takwa, ya ce: “A cikin daren ranar Talata 11 ga watan Janairu, 2022, sojoji sun samu kiran kai hari kan al’ummar Ancha.

 

“Rundunar sojojin sun mayar da martani cikin gaggawa sannan suka yi gangami zuwa kauyen. Da isar su yankin, maharan sun gudu. An lalata gidaje tare da rasa rayukansu a yayin harin.''

 

"Sojoji suna kan bin maharan kuma za a fitar da cikakkun bayanai game da lamarin."

 

Kwamandan rundunar ‘Operation Safe Haven’ I. S Ali, wanda ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, ya bada tabbacin cewa za’a kama wadanda suka aikata wannan aika-aika.

 

Gwamna Simon Bako Lalong ya bayyana bakin cikinsa game da harin, inda ya ce wannan labari ne mai ban tausayi a cikin tashe tashen hankula da yaki karewa a yankin.

 

Jarida Radio

13/1/2022

COMMENTS
Comment sent successfully!