Volume
Offline Radio
Social
Networks
Hukumar EFCC ta kama Janar din sojan bogi da yace an nada shi babban hafsan soji.
01/13/2022 18:57 in Najeriya

 

Aliyu Samba

Hukumar EFCC ta kama Janar din sojan karya wanda ya yi ikirarin Buhari ya bada sunan shi a matsayin Babban Hafsan Soji bisa zargin almundahanar N270m

 Jami’an hukumar EFCC shiyyar Legas sun kama wani mai suna Bolarinwa Oluwasegun, Janar na sojan bogi bisa zarginsa da damfarar N270m.

Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta wallafa a shafin ya na facebook a yammacin ranar Alhamis. 

 Wanda ake zargin, wanda ya bayyana kansa a matsayin Janar a rundunar sojojin Najeriya, ya yi karyar cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tantance shi da wani daya da za a nada a matsayin shugaban hafsan sojin kasa, COAS, kuma yana buƙatar wasu kuɗaɗe dan gudanar da shirye-shiryen sa kan matsayin da aka naɗa shi. 

Sannan kuma yayi takardar ƙarya dake nuna an naɗa shi a matsayin Babban Hafsan Soji da sa hannun ƙarya da akai da sunan Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

 

Jarida Radio

13/1/2022

 

COMMENTS
Comment sent successfully!