Volume
Offline Radio
Social
Networks
Kotun kolin Amurka ta hana tilasta allurar Korona
01/14/2022 09:55 in Kiwon Lafiya

Kotun Ƙolin Amurka ta yi watsi da umarnin da Shugaba Joe Biden ya bayar da ya tilasta wa ma'aikata yin rigakafin annobar korona a manyan kamfanoni.

Kazalika umarnin ya tilasta saka takunkumi da kuma yi wa ma'aikatan gwaji a duk mako.

Alƙalan kotun sun ce umarnin ya shallake ƙarfin ikon da shugaban ƙasar ke da shi.

Sai dai sun yanke hukuncin cewa za a iya ba da wani umarnin maras tsauri na yin rigakafi ga ma'aikata a asibocin gwamnati.

Gwamnatin Biden ta dage kan cewa tilashin zai taimaka wajen yaƙi da cutar.

Shugaba Biden wanda farin jininsa ke raguwa a ƙasar, ya bayyana rashin jin daɗinsa da hukuncin da ya "daƙile tunani mafi sauƙi da zai kare rayuwar ɗan Adam ga ma'aikata".

Ya ƙara da cewa: "Ina kira ga jagororin 'yan kasuwa da su yi koyi da waɗanda suka ɗauki matakai - ciki har da ɗaya bisa uku na kamfanonin Fortune 100 - don su kare ma'aikatansu da kwastomi da jama'ar yankunansu." 

Tushe: BBC Hausa 14/01/2022

COMMENTS
Comment sent successfully!