Nijeriya

Yanzu Trump ya yarda ana kashe Musulmai a Najeriya

Trump ya yarda ana kashe Musulmai a Najeriya

A karon farko tun bayan da Shugaba Donald Trump ya karkata akalarsa kan rashin tsaro a Najeriya, ya amince cewa ana kashe Musulmai suma.

Sai dai a wata hira da jaridar New York Times, Trump ya amince cewa babu mabiya addinin da abin bai shafa ba, amma ko a wancan lokacin ya yi ikirarin cewa Kiristoci abin ya fi shafa.

Bayan harin da Amurka ta aki ranar Kirsimeti kan sansanin ‘yanta’adda a jihar Sokoto, Trump ya ce za a iya samun karin hare-hare daga Amurka.

Sai dai da aka tambayi mai bai wa Trump shawara a Afirka ya ce mayakan IS da Boko Haram suna kashe Musulmai fiye da Kiristoci. Trump ya mayar da martani da cewa: “Ina tsammanin ana kashe Musulmi ma a Najeriya. Amma yawancin Kiristoci ne wadanda aka fi kashewa.”

Trump, a karshen watan Oktoba, ya fara gargadin cewa addinin Kiristanci na fuskantar “barazana” a Najeriya tare da yin barazanar shiga tsakani ta hanyar soji kan abin da ya alakanta da gazawar gwamnati na dakatar da tashe-tashen hankula.

Trump ya sake mayar da Najeriya a matsayin kasar da ake sa wa ido kan addinin Musulunci, ya kuma zargi gwamnati da rashin mayar da hankali wajen kare rayukan al’umma.

Sai dai daga baya gwamnatin tarayya ta aika da wata tawaga mai karfi zuwa kasar Amurka domin bayyana halin da tsaron Najeriya ke ciki. Bayan ziyarar, manyan jami’an Amurka sun kuma ziyarci Najeriya domin ganewa idanunsu halin da ake ciki.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button