‘Yan bindiga sun sace matafiya 18 amma an ceto 11
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da matafiya 18 an ceto 11

Rundunar ‘yan sanda ta ceto fasinjoji 11 cikin 18 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a hanyar Benin zuwa Akure kusa da kauyen Obarenren a karamar hukumar Ovia ta Arewa maso Gabashin jihar Edo a ranar 12 ga watan Disamba.
Maharan dauke da manyan makamai sun tilasta wa motar tsayawa da bindiga, inda suka rika harbe-harbe tare da tasa keyar matafiyan cikin daji.
Da take tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Edo, ASP Eno Ikoedem, ta shaida wa Jarida Radio cewa, rundunar ta samu kiran gaggawa jim kadan bayan harin, inda nan take ta tattara jami’an tsaro tare da hadin gwiwar sojoji da ‘yan banga da mafarauta sun kaddamar da aikin bin sahun ‘yan ta’addan a dajin domin kamo masu garkuwa da mutanen tare da kubutar da wadanda lamarin ya shafa.
ASP Ikoedem ta tabbatar da cewa ‘yan sanda suna yin duk mai yiwuwa don ganin an sako sauran wadanda abin ya shafa.
Ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankulansu tare da ba jami’an tsaro hadin kai, da bayyana kwarin gwiwar cewa za a kubutar da sauran fasinjojin da aka sace ba tare da wani rauni ba.




