Nijeriya

Ba za mu yi maja ba – SDP

Jam'iyyar SDP a Najeriya ta yi watsi da yunkurin haɗaka

Jam’iyyar SDP a Najeriya ta yi watsi da yunkurin haɗaka tsakaninta da sauran jam’iyyun adawa da nufin tunkarar zaɓen 2027.

Wannan na zuwa yayin da ake ganin tagomashin jam’iyyar ta SDP ya karu sakamakon sauya shekar da wasu manya ‘yan siyasa a kasar ke yi zuwa cikinta

A makon da ya gabata ne wasu jagororin adawa ƙarƙashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP suka sanar da cewa suna wani yunƙuri na ƙulla haɗaka domin kawar da APC a zaɓen 2027.

Sai dai shugaban jam’iyyar na kasa Alhaji Shehu Musa Gabam a hirarsa da BBC ya ce SDP ba za ta haɗe da wata jam’iyya ba.

Majiya @bbchausa

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button