Nijeriya
Yanzu-yanzu: APC ta lashe kananan hukumomi 20 na Ribas
APC ta lashe kananan hukumomi 20 cikin 23 na Ribas

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta lashe kananan hukumomi 20 cikin 23 a zaben kansiloli da aka gudanar a ranar Asabar.
A daya bangaren kuma, jam’iyyar PDP wadda ita ce jam’iyya mai mulki kafin ayyana dokar ta-baci a watan Maris, ta lashe kananan hukumomi uku ne kacal a zaben.
Shugaban Hukumar Zaben Jihar Ribas (RSIEC) Dr. Michael Odey ne ya sanar da sakamakon a hedikwatar hukumar da ke Fatakwal a yammacin Lahadi.
Dr. Michael Odey ya kuma bayyana sunayen wadanda suka lashe zaben mataimakin shugaban kasa, sai dai kawo yanzu ba a bayyana sakamakon zaben kansilolin ba.