Kungiyar ma’aikatan mai a Najeriya ta ba da umarni kan matatar Dangote sakamakon korar jama’a
Kungiyar mai a Najeriya ta ba da umarnin dakatar da samar da iskar gas ga matatar Dangote sakamakon korar jama'a

Kungiyar ma’aikatan man fetur a Najeriya ta umarci mambobinta da su katse iskar gas da ake samarwa matatar man Dangote, bayan korar daruruwan ma’aikata.
Kungiyar manyan ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta umurci rassa a manyan kamfanonin mai da su tilasta dakatar da kai danyen mai da iskar gas zuwa matatar.
Kungiyar ta zargi mahukuntan Dangote da “lalata da farfaganda” maimakon su magance zargin korar ma’aikatan kungiyar ba bisa ka’ida ba, kamar yadda wata wasika mai dauke da kwanan watan Satumba 26 da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.
Matatar man Dangote ta ce a ranar Juma’a ta kori wasu tsirarun ma’aikata, sakamakon zagon kasa da aka samu a sassa daban-daban. Hakan dai ya janyo suka daga kungiyar ma’aikatan mai da ta ce an kori ma’aikatan Najeriya sama da 800 tare da zargin an maye gurbinsu da wasu ‘yan kasashen waje galibi ‘yan kasar Indiya.
RIKICIN YANA KARA MATSALAR MATATAR DANGOTE
“Ya kamata a rufe bawuloli da ke samar da danyen mai a matatar” sannan aka dakatar da lodin tasoshin da za su nufi wurin nan take, kamar yadda babban sakataren PENGASSAN Lumumba Okugbawa ya rubuta.
Matatar man Dangote ta ce korar da aka yi wani bangare ne na sake tsarawa domin inganta tsaro.
A ranar Asabar din da ta gabata ta ce, “babu wata doka da ta bai wa PENGASSAN ‘yancin umurtar rassanta da su ‘katse’ iskar gas da danyen mai ga matatar Dangote, ko kuma ta yi katsalandan ko tada kayar baya a kwangilar da take yi da dillalai da masu kaya.
Rikicin dai ya kara matsin lamba kan matatar mai da ta kai dalar Amurka biliyan 20, wadda ta ce za ta dakatar da sayar da man fetur a naira daga ranar 28 ga watan Satumba saboda karancin danyen mai da kuma rashin daidaiton kudaden waje. Matakin dai ya haifar da fargabar hauhawar farashin man fetur da kuma kara tabarbarewar kudin Najeriya.