
An rantsar da Netumbo Nandi-Ndaitwah a matsayin mace ta farko da ta zama shugabar kasar Namibiya, bayan da ta lashe zabe a bara wanda ya tsawaita wa’adin jam’iyya mai mulki na shekaru 35.

Nandi-Ndaitwah, mai shekaru 72, ta kasance daya daga cikin shugabanni mata kalilan a nahiyar Afirka, bayan gudanar da bikin mika mulki a ranar Juma’a da ya samu halartar shugabannin kasashen Afirka da dama da suka hada da Angola, Afirka ta Kudu da Tanzania.
A jawabinta na farko, Nandi-Ndaitwah ta amince da zabenta mai cike da tarihi, amma kuma ta ce ‘yan Namibiya sun zabe ta ne saboda cancanta da cancantarta.
Ta kara da cewa duk da cewa kasar ta samu ci gaba tun bayan samun ‘yancin kai, “akwai abubuwa da yawa da ya kamata a yi.”