Nijeriya

Atiku da Peter Obi na tattaunawa kan yiwar hadewa a SDP

Atiku da Peter Obi na tattaunawa kan yiwar hadewa

A wani mataki da ka iya sauya fasalin ‘yan adawar siyasa a Nijeriya, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP a 2023, Prince Adewole Adebayo, ya tabbatar da cewa ana tattaunawa ta farko da Atiku Abubakar da Peter Obi kan yiwuwar shiga jam’iyyar Social Democratic Party.

Da yake magana da jaridar Sunday Politics, Adebayo ya fayyace cewa duk da cewa ba a samu matsaya ba ana tattaunawa da sauran abokan siyasa. Ya kuma jaddada cewa SDP na maraba da wadanda suka gamsu da manufofinta na adalci a zamantakewa, gyara dimokuradiyya, da hadin kan kasa.

Wannan batun na zuwa ne ana tsaka da rikicin cikin gida a jam’iyyun PDP da Labour bayan zaben 2023. Masu sharhi dai na nuni da yuwuwar daidaitawar Atiku-Obi a karkashin jam’iyyar SDP zai iya sauya ma’auni na siyasa sosai kafin 2027.

Ko da yake babu wanda ya yi magana a bainar jama’a a cikinsu, tarurrukan bayan fage da kuma shirun da suka yi a kafofin watsa labarai suna nuni ga sauye-sauyen dabaru.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button