Nijeriya

El-Rufai: Za mu iya cin nasara ba tare da gwamnoni ba

Za mu iya cin nasara ba tare da gwamnoni ba - El-Rufai

Wani jigo a hadakar jam’iyyun adawa da ke kunno kai, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa kungiyar ba ta bukatar goyon bayan gwamnoni don tsige shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Da yake magana a lokacin da yake zantawa da manema labarai jiya a Kano, tsohon gwamnan jihar Kaduna – wanda ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) – ya ce dabarun kungiyar sun fi mayar da hankali ne wajen tara masu kada kuri’a kai tsaye, ba zawarcin masu rike da mukaman siyasa ba.

Kalaman El-Rufa’i sun zo ne a kan koma bayan kungiyar gwamnonin PDP na kin amincewa da duk wani hadin kai ko hadewa kafin 2027.

Bayan ziyarar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2023 ya kai wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Kaduna, tare da ‘yan jam’iyyar hadin gwiwa da suka hada da El-Rufai, an yi ta rade-radin cewa gwamnonin PDP za su yi hannun riga da sabuwar kungiyar adawa.

Sai dai bayan wani taro da aka yi a Ibadan – wanda ya samu halartar mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Ambasada Umar Damagum, da wasu gwamnoni da dama – kungiyar ta nisanta kanta daga yunkurin hadin gwiwa.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button