Wasanni

Ghana ta yi nisa wajen samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya

Ghana ta ci Madagascar 3-0

Dan wasan Ghana Thomas Partey ne ya zura kwallaye biyu sannan Mohammed Kudus ya kara daya yayin da kungiyarsu ta samu nasara a kan Madagascar da ci 3-0 ranar Litinin a Morocco a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a shekara mai zuwa.

Ghana dai ba ta samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a shekarar 2025 ba, bayan da ta yi rashin nasara a gasar da ta gabata wanda ya ba da mamaki. Amma ta yi nisa wajen samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya mai kasashe 48 da za a yi a Amurka da Mexico da kuma Canada.

Suna da maki 15 daga wasanni shida a rukuni na daya, da maki biyar a gaban Madagascar da ke matsayi na biyu, yayin da Mali ke matsayi na uku da maki 6.

 

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button