Nijeriya
Gwamna Yusuf yayi barazanar kwace gidaje a Kwankwasiyya, Amana, Bandirawo

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayar da umarnin zartarwa da ya umarci masu gidajen da ke rukunin Kwankwasiyya, Amana, da Bandirawo da su tare a gidajensu nan da watanni uku ko kuma su fuskanci kwacewa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin
Umarnin ya biyo bayan rantsar da sabon kwamishinan raya gidaje a fadar gwamnatin Kano.
Ya kuma bukaci wadanda ba za su iya kaura ba da su yi la’akari da bayar da hayar gidajensu, yana mai jaddada kudirin gwamnati na ganin rukunin gidajen sun bunkasa.