Nijeriya
Jihar Edo: An dakatar da shugaban lafiya a matakin farko na jihar
An dakatar da shugaban lafiya a matakin farko na jihar Edo

Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya bayar da umarnin dakatar da babban sakataren hukumar kula da lafiya matakin farko na jihar Edo, Dr. Caulson Osoikhia Oahimire.
Gwamnan ya kuma ce za a kafa kwamiti na musamman da zai binciki shugaban da aka dakatar.
Gwamnan a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Musa Ikhilor ya fitar, ya ce an dakatar da Oahimire ne bisa zarge-zargen kan badakalar makudan kudade da kuma wasu ayyuka na hukuma.