Wasanni
Karawar Tawagar Nijeriya da Zimbabwe
Najeriya za ta buƙaci ta samu maki uku a wasanta da Zimbabwe

A yammacin yau Talata ne Najeriya za ta karɓi baƙuncin Zimbabwe domin buga wasan ta karo na 6 na neman gurbin shiga gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya na 2026.
Mai horas da tawagar ƙwallon kafa ta Najeriya Eric Chelle ya fara jan ragamar ƙungiyar da ƙafar dama, inda ya yi nasarar ci 2-0 kan ƙungiyar ƙwallon kafa ta Rwanda a wasansa na farko. Victor Osimhen ya zura ƙwallaye biyu a wasan wanda ya kai su ga samun maki uku.
Najeriya za ta buƙaci ta samu maki uku a wasanta da Zimbabwe wadda suka tashi 2-2 da ƙasar Benin, kuma a yanzu tana matsayi na shida a rukunin C.