Nijeriya

Kazanta Ta Yi Wa Legas Katutu – Jam’iyyun Adawa

Wannan suka dai na zuwa ne bayan mazauna yankuna da dama sun bayyana damuwarsu a shafukan sada zumunta musamman ta manhajar x.com

Wannan suka dai na zuwa ne bayan mazauna yankuna da dama sun bayyana damuwarsu a shafukan sada zumunta musamman ta manhajar x.com game da wannan warin. Wuraren da suka hada da Iyana Iba da Igando Oko Filling da Ojota da karkashin gadar Ajah  duk an bayyana su wurare na musamman wadanda warin ya shafa.

Jam’iyyar PDP da Labour duk sun caccaki gwamnatin jihar Legas
karkashin jam’iyyar APC kan korafe-korafen da ake yi na wari da ke tashi daga sassan birnin.

 

Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na Legas, Tai Benedict, ya bukaci gwamnatin jihar da ta dauki matakin gaggawa, wajen inganta tsafta saboda illolin da rashin ta ka iya haifarwa. Ya ci gaba da cewa, “Ya kamata gwamnatin APC ta taimaka mana wajen fitar da wannan mummunar wari da ya addabemu.

Gbadebo Rhodes-Vivour, dan takarar gwamnan jihar Legas na jam’iyyar Labour a 2023, ya soki yadda jihar ke tafiyar da sharar gidaje da rashin samar da rumbunan shara a yankunan kwaryar cikin garin Legas. Ya ba da shawarar hanyoyin da za a bi, kamar inganta ingancin iska ta hanyar dashen bishiya. Ya kuma jaddada bukatar samar da ingantattun hanyoyin magance matsalolin magunan ruwa a cikin birnin.

A martanin da mai magana da yawun jam’iyyar APC na Legas, Seye Oladejo ya yi, ya yi watsi da sukar ‘yan adawar da cewa yana da alaka da siyasa, inda ya nuna cewa suna neman uzuri ne maimakon mafita.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button