Wasanni

Fenerbahce ta kori kocinta Jose Mourinho

Kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya ta kori kocinta Jose Mourinho

Kungiyar Fenerbahce ta Turkiyya ta raba gari da kocinta Jose Mourinho, kamar yadda kungiyar ta sanar a ranar Juma’a.

“Mun rabu da Jose Mourinho, wanda ya kasance manajan kungiyar kwallon kafarmu tun daga kakar wasa ta 2024-2025. Muna gode masa kan kokarin da ya yi a kungiyarmu kuma muna masa fatan samun nasara a rayuwarsa,” in ji Fenerbahce a cikin wata sanarwa.

An dauki matakin ne kwanaki biyu bayan da kungiyar ta Fenerbahce ta fitar da Benfica daga gasar cin kofin zakarun Turai.

Mourinho, kocin dan kasar Portugal wanda ya yi fice a gasar cin kofin nahiyar Turai, ya samu nasara sau 37, kunnen doki 14 da rashin nasara 11 a wasanni 62 da ya buga da Fenerbahce.

Rigingimu

Tsohon kocin na Chelsea, Real Madrid, Inter Milan, Manchester United, Tottenham Hotspur da kuma Roma wanda ya isa kulob din Fenerbahce a watan Yunin 2024, ya jagoranci kungiyar Yellow Canaries ta Istanbul zuwa matsayi na biyu a gasar bara bayan Galatasaray, inda suka kasa kawo karshen matsalar rashin kambun gasar.

Kocin mai shekaru 62 a duniya ya samu koma baya da dama a zamansa a Istanbul. A watan Afrilu, ya dakumi fuskar kocin Okan Buruk a gaban abokan hamayyarsa na gida Galatasaray bayan da suka sha kashi da ci 2-1 a gasar cin kofin Turkiyya, inda ya murza hanci.

An kuma ci tarar shi ne saboda kalaman da ya yi bayan wani fafatawar da suka yi da Galatasaray, inda ya kuma maimaita sukar alkalan wasan Turkiyya, inda ya zargi alkalin wasa na hudu da nuna son kai. An yi la’akari da kalaman nasa da cewa “ya saba wa ka’idojin wasanni”.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button