
DAGA ADAMU ALIYU NGULDE, MAIDUGURI
A ranar Asabar din da ta gabata ne wata yarinya ‘yar shekara 15 ta gamu da ajalinta a birnin Maiduguri, na jihar Borno bayan da wani jami’in sa kai na ‘Civilian Joint Task Force (CJTF)’ ya matsa kunamar bindiga bisa kuskure ya harbe ta.
Majiyoyi sun shaidawa ‘Jarida Rediyo’ cewa lamarin ya faru ne a unguwar Kanti Goma Shabiyu na unguwar Umarari da ke kan titin Baga, yayin da jami’an CJTF da ke aiki a yankin suka yi yunkurin kama wanda ya yi harbin bisa kuskure.
Wani mai suna Abba Sidi Mala mai shekaru 27 ya fitar da bindiga cikin bazata kuma ya matsa kunamar bindigar wanda hakanne ya yi sanadiyar raunata kan Zainab Usman.
A halin yanzu dai tawagar jami’an tsaro da ke sintiri sun yi gaggawar kai agaji sannan sun dauki Zainab zuwa Asibitin kwararru na jiha, (State Specialist Hospital) inda aka tabbatar da mutuwar ta.
Hakazalika jami’an asibitin sun mika wa iyayen Zainab gawar marigayiyar domin yin sutura a binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa ‘yan sanda sun kama wanda ake zargin, kuma a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.