Manchester United ta yi karin farashin tikitin kallon wasa

Manchester United ta sanar a ranar Litinin da ta gabata da karin kusan kashi 5% a farashin tikitin kallon wasannin kakar bana a Old Trafford na shekarar 2025-26 a wani sabon yunƙuri na magance matsalolin kuɗin da kulob din na Premier ke fuskanta.
Farashin tikitin wasannin maza zai karu da matsakaicin fam 2.50 ($3.25), ban da ‘yan kasa da shekaru 16. United tana mataki na 13 a teburin gasar Premier kuma dubban magoya bayanta sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin amincewa da shugabannin kungiyar a farkon wannan watan.
Kungiyar magoya bayan Manchester United (MUST) ta ce karin farashin tikitin na baya-bayan nan ya yi kasa da yadda mutane da yawa ke sa rai, amma sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda kulob din ya yi watsi da kiran da aka yi na rage farashin tikitin.
Bayan da United ta sanar da rage ma’aikata 150 zuwa 200 a watan da ya gabata, a makon da ya gabata United ta bayyana shirin gina sabon filin wasa mai daukar kujeru 100,000, wanda zai kasance mafi girma a Biritaniya.
Bashin da United ke bin a halin yanzu, wanda ya hada da fam miliyan 300 na cikin musayar yan wasa, ya haura fam biliyan daya.