
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya fada a ranar litinin cewa kasarsa ta yi asarar kudaden shiga na mashigar ruwa ta Suez wadda ta kai kusan dalar Amurka miliyan 800 saboda halin da ake ciki a yankin, yayin da ‘yan Houthi na kasar Yemen ke kai hare-hare kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya.
Tun a watan Nuwamban shekarar 2023 ne mayakan Houthis suke kai hari kan jiragen ruwa a yankin tekun Bahar Rum, domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a Gaza, kan yakin da Isra’ila ke yi, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin sufurin jiragen ruwa a duniya, ta hanyar tilastawa jiragen ruwa gujewa mashigin Suez da ke kusa da su, da kuma durkutsar da harkokin kasuwanci a nahiyar Afirka, lamarin da ya kara tsadar sufuri.
Sanarwar da fadar shugaban Masar ta fitar ba ta yi nuni da Houthis kai tsaye ba, amma Sisi ya ce a watan Disambar bara ta janyo wa Masar asarar kusan dala biliyan 7 na kudaden shiga daga kogin Suez a shekarar 2024.
A baya-bayan nan ne kungiyar ta Yemen ta lashi takobin ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan Amurka a tekun Bahar Maliya, a matsayin martani ga munanan hare-haren da Amurka ta kai kan kasar Yemen, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 53 a ranar Asabar, a farmakin da sojojin Amurka suka kai a yankin gabas ta tsakiya mafi girma tun bayan da shugaba Donald Trump ya hau karagar mulki a watan Janairu.
Sun kuma ce a makon da ya gabata za su ci gaba da kai hare-hare kan jiragen ruwan Isra’ila da ke wucewa ta tekun Bahar Rum idan Isra’ila ba ta dage shingen da ta kakaba na shiga Gaza ba.