Afirka

Mayakan Somaliya sun kai harin bam kan ayarin motocin shugaban kasar

Kungiyar ta’addancin nan ta Al Shabaab ta sanar da cewa, mayakanta sun kaiwa shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud hari, a wani harin bam kan ayarin motocinsa, a lokacin da suke tafiya a cikin babban birnin kasar Mogadishu a ranar Talata.

Wasu manyan jami’an gwamnati da na soji biyu sun shaida wa kamfanin dillancin labaran reuters cewa Mohamud na cikin koshin lafiya bayan harin, kuma mai baiwa shugaban kasar shawara Zakariye Hussein ya rubuta a wani sako da ya wallafa a shafin X cewa yana cikin koshin lafiya.

Sojoji da mazauna yankin da suka shaida harin sun tabbatar da cewa an kai wa ayarin motocin shugaban hari. Wani dan jarida na Reuters a wurin ya ga gawarwakin mutane hudu da aka kashe a harin da aka kai kusa da fadar shugaban kasar.

“Mayakan mu sun kai hari kan ayarin motocin da ke dauke da Hassan Sheikh Mohamud a lokacin da suke fitowa daga fadar shugaban kasa zuwa filin jiragin sama,” in ji kungiyar ta al-Shabaab a cikin wata sanarwa da ta wallafa a wani shafin manhajar Telegram na kungiyar mai alaka da al-Qaeda.

Yayin da al-Shabaab ke kai hare-hare a Somaliya a wani bangare na yakin da ta kwashe shekaru da dama tana yi na hambarar da gwamnatin kasar, harin na ranar Talata shi ne na farko da ta kai kai tsaye ga Mohamud tun shekara ta 2014, a wa’adin mulkinsa na farko, lokacin da suka kai harin bam a wani otel da yake magana.

Sa’o’i kadan bayan harin da aka kai a ranar Talata, kafofin yada labaran kasar sun nuna hotunan shugaban a gundumar Adan Yabal da ke yankin Shabel ta Tsakiya na kasar Somaliya, inda dakarun gwamnati ke fafatawa da wani harin na tsawon makonni uku na kungiyar Al Shabaab.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button