
Naira Marley fitaccen mawakin Nijeriya ya kan bayyana addininsa na musulunci a karara, ta hanyar wallafa abubuwan da suka shafi musulunci a shafukan sada zumunta musamman a watan ramadan.
Sai dai mawakin wanda yawanci ya kan sirka batsa a wakokinsa, dalilin da ya sa ya ke shan raddi da suka daga al’umma da mabiyansa masu mabanbantan ra’ayin addini, la’akari da yadda ya ke kame kansa a watan ramadan wanda hakan ke sosa musu rai.
Ya yi kira da a daina alankanta kurakuren da ya ke tafkawa da addininsa ”A dina danganta addinina na musulunci da kuskuren da nake yi, abunda nake yi mai kyau daga addinina ne, amma saɓanin haka to daga ajizanci ne irin nawa na Adam… – inji mawaƙi Naira Marley
Mawaƙi Naira Marley ya ce “A daina danganta kuskuren da nake yi da addinin musulunci… Shi addinin musulunci rahama ne domin addini ne na Allah. A matsayina na musulmi dan Adam ne ajizi ne dole ina kuskure, don haka kuskure nawa ne ba na addini na ba”