
Rwanda ta ce a ranar Litinin din nan ta yanke huldar diflomasiyya da Belgium tare da korar dukkan jami’an diflomasiyyarsu, a daidai lokacin da alakar da ke tsakaninta da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango ta yi tsami.
Ministan Harkokin Wajen Belgium Maxime Prevot ya ce, “Belgium ta yi nadamar shawarar da Rwanda ta yanke na yanke huldar diflomasiyya da Belgium tare da bayyana jami’an diflomasiyyar Belgium wadanda ba su dace ba.”
“Wannan bai dace ba kuma yana nuna cewa idan muka yi rashin jituwa da Rwanda sun gwammace kada su shiga tattaunawa.”