Duniya

Sabon bututun iskar gas daga Rasha zuwa China – Putin

Yana cikin manyan ayyukan makamashi a duniya

Rasha da China sun rattaba hannu kan yarjejeniyar gina bututun mai a ziyarar da Putin ya kai China a wannan mako, amma kamfanin makamashi na Rasha Gazprom, wanda ke da niyyar fara isar da iskar gas ta bututun nan da shekara ta 2030, ya ce har yanzu ba a amince da farashin ba.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a ranar Juma’a 5 ga watan Satumba yace, shirin sabon bututun iskar gas na Siberiya 2 zuwa kasar China, wani aiki ne da za a mora tare, kuma farashin iskar gas din zai dogara ne kan tsarin kasuwa kamar yadda da Rasha ta saba samarwa kasashen Turai kafin yakin Ukraine a 2022.

Shugaban Rasha Vladimir Putin (D) and Shugaban China Xi Jinping sun gaisa bayan rattaba hannu a kan yarjejeniya

“Wannan shi ne daya daga cikin manyan ayyukan makamashi a duniya,” in ji Putin, yayin da yake magana a wani taron tattalin arziki a Vladivostok.

Ya ce “za a kididdige farashin ta hanyar amfani da ainihin tsari iri ɗaya na jigilar kayayyaki zuwa Turai … Yana da cikakken kasuwa.”

Kasar Rasha dai ta yi hasarar mafi yawan kasuwar iskar gas a Turai tun bayan fara yakin Ukraine.

Firayim Ministan Mongoliya Zandanshatar Gombojav, wanda sabon bututun mai zai bi ta kasarsa, ya shaida wa wannan taron cewa Ulaanbaatar a shirye yake ya ci gaba da aiki amma akwai cikakkun bayanai da za a yi aiki.

Mongoliya na iya sayen wasu iskar gas na Rasha, in ji shi.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button