
Fulham ta sayi dan wasan Najeriya Samuel Chukwueze daga AC Milan a matsayin aro tare da zabin siyan €26 miliyan ($ 30.2 miliyan.
Da wannan yarjejeniya Chukwueze zai bi sahun sauran taurarin Najeriya Alex Iwobi da Calvin Bassey a Fulham.
An sanya sunan Chukwueze a cikin ‘yan wasan Najeriya da za su buga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za su kara da Rwanda da Afirka ta Kudu a cikin kwanaki masu zuwa.