Nijeriya

Sojojin Sun Kama Masu Garkuwa da Mutane a Jihar Filato

A ranar 15 ga Maris, 2025, dakarun Operation SAFE HAVEN sun yi wani gagarumin nasara inda suka kama wasu mashahuran masu garkuwa da mutane, Bashir Mohammed da Ismail Mohammad, a jihar Filato.

Rundunar tare da Operation LAFIYAN JAMA’A ta gudanar da wani samame ne a maboyar masu garkuwa da mutane a saman tudun Katume dake karamar hukumar Bassa, sakamakon samun sahihan bayanai da ke nuna cewa masu garkuwa da mutane kan boye wadanda aka sace a yankin yayin da suke tattaunawa don neman kudin fansa.

A yayin samamen sojojin sun kwato bindiga kirar AK-47 guda daya da harsashin AK-47 daya daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Masu garkuwa da mutanen da aka kama a halin yanzu suna tsare, inda suka bayar da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen gudanar da ayyukan da za a bi domin kamo ‘yan kungiyarsu tare da kwato makamansu.

Wannan nasarar dai wata shaida ce da ke nuna irin tasirin da kokarin da Operation SAFE HAVEN ke yi na magance matsalar rashin tsaro a yankin.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button