
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani jawabi da aka watsa a fadin kasar a daren ranar Talata.
Ya alakanta faruwar lamarin da tashe-tashen hankula a jihar, inda ya ce ‘yan bindiga sun fasa bututun mai da dama.
Tinubu ya ce Gwamna Siminalayi Fubara ko mataimakiyarsa ba su kai masa rahoto a lokacin tashin hankalin ba, kuma ba zai nade hannayensa ya bari lamarin ya tabarbare.