Nijeriya

Yadda ake huce haushin Fulani kan Hausawa

Huce haushin Fulani kan Hausawa

Ba a gama fita daga cikin alhinin kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya 12 ’yan Jihar Kaduna a Jihar Filato ba, sai aka kara samun wani labarin kisan wasu mutum biyu ’yan Jihar Kano wadanda su kuma aka kashe a garin Makurdi a Jihar Binuwe ranar Litinin.

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi Allah wadai da kisan kuma ya bayyana shi da “aikin dabbanci wanda ba za a taba lamunta ba”. Sannan ya bukaci jami’an tsaro da su tabbatar an hukunta wadanda suka aikata kisan, kamar yadda mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Shi ma gwamnan jihar ta Binuwe Rebaran Hyacinth Alia ya yi Allah wadai da kisan, yana bayyana shi a matsayin dabbanci, sannan ya ce tuni aka kama mutum biyar da ake zargi suna da hannu a kisan, kamar yadda kakakinsa Sir Tersoo Kula ya bayyana a wata sanarwa.

Makamancin irin wannan kisan gillar

Idan za a tuna a karshen watan Maris an yi wa wasu ’yan arewacin kasar mafarauta mummunan kisan gilla a garin Uromi na Jihar Edo yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida yin bikin karamar sallah.

A cikin wani bidiyo da aka rika yadawa a intanet a lokacin, an ga yadda gungun mutanen suka yi wa mafarautan dukan kawo wuƙa sannan suka cinna musu wuta suka ƙona su ƙurmus.

A duk lokacin da aka yi irin wannan kisa dai, jama’a na sake jaddada kiraye-kiraye ga gwamnati da a dauki mataki kan duk wadanda suke da hannu a irin wadannan ta’addanci, yayin da a bangare guda kuma wasu suke zargin gwamnatin da kasa daƙile irin wadannan kashe-kashen na ɗaukar doka a hannu wanda yake yawan faruwa a Nijeriya.

Mece ce mafita?

Mai sharhi kan harkokin tsaro kuma satakare janar na kungiyar tsofaffin sojojin Nijeriya Dokta Auwal Abdullahi Aliyu ya ce ramuwar gayya da takalar husuma da dalilan siyasa ne manyan abubuwan da suke jawo irin wadannan munanan kashe-kashe wadanda ake yi wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Masanin tsaron ya ce mutanen jihohin Binuwe da Filato suna zargin al’ummar Fulani da kashe-kashe da kuma batun cewa sun zama ’yan kama wuri zauna a jihohinsu. Sannan ya ce akwai matsalar rikicin makiyaya da manoma da ta garkuwa da mutane wadanda su ma suke kara rura wutar rashin yarda da haddasa husuma a kasar.

Dakta Auwal ya ce mutanen Binuwe da Filato suna zargin Fulani ne ke kashe-kashen da ake yi a jihohinsu, duk da babu tabbas kan hakan, amma mutanen jihohin suna yin kudin goro kan duk wani Bahaushe, su dauki doka a hannu, kuma su yi masa kisan gilla.

Masanin ya ce za a iya magance wadannan matsaloli ne ta hanyar tattaunawa da wayar da kai da nuna wa mutane illolin rashin zaman lafiya da kuma uwa uba hukunta wadanda suka aikata munanan ayyukan don hakan ya zama darasi ga duk wani da ke son aikata hakan a gaba.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button