Nijeriya

Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kama gungun ‘yan tadda 13

‘Yan sandan sun yi galaba a kan 'yan taddan da ke dauke da makamai

A wata ganawa da manema labarai a babban hedikwatar ‘yan sandan Nijeriya a Abuja kan kwazon aiki, jami’an rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta bayyana wa Jarida Radio cewa ta gudanar da ayyuka da dama da suka hada da jajircewa wajen tabbatar da cewa rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta dauki matakin inganta tsaro a cikin gida da kuma yaki da miyagun ayyuka a fadin kasar.

A ranar 11 ga Maris, 2025, jami’an hukumar ‘Intelligence Response Team (IRT)’ na kan hanyarsu ta zuwa jihar Edo ne suka ci karo da wani kwanton bauna da wasu ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane suka yi a Oshara Ganden da ke kan iyakar jihohin Kogi da Edo.

‘Yan sandan sun yi galaba a kan ‘yan taddan da ke dauke da makamai, lamarin da ya sa aka kama mutane takwas.

Wadanda ake zargin, an same su da bindiga kirar AK-47 guda daya dauke da alburusai 29, bindiga kirar pump action 6, bindiga kirar short gun 2 da baburai.

Wannan aikin da suka yi cikin nasara ya nuna irin jajircewar da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ke yi wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

An yi kira ga ‘yan kasar da su baiwa ‘yan sanda goyon baya ta hanyar ba da sahihan bayanai kan lokaci, domin hadin kan su na da matukar muhimmanci wajen yaki da masu tafka miyagun laifuka.

Majiya: ACP OLUMUYIWA ADEJOBI
Jami’in Hulda da Jama’a na Hedikwatar ‘Yan sanda na Abuja

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button