NijeriyaUncategorized

Mayaƙan ISWAP sun tarwatsa gada a Yobe

Mayaƙan ISWAP sun tarwatsa gada a Arewa maso gabashin Nijeriya

Daga Adamu Aliyu Ngulde

Wasu da ake kyautata zaton mayaķan ISWAP sun tarwatsa wata gada da ta haɗa garin Ngirbuwa da garin Goneri na karamar hukumar Gujiba da ke Jihar Yobe da ke yankin Arewa maso gabashin Nijeriya.

Wannan na zuwa ne kwanaki takwas da ‘yan ta’addan suka lalata gadar nan ta Mandafuna da ta haɗa karamar hukumar Biu da Damboa a jihar Borno.

Majiyar leƙen asiri ta shaida wa ‘Jarida Radio’ cewa harin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na daren ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ta hanyar amfani da wani bam wajen lalata sauran sassan gadar domin kawo cikas ga matafiya.

A halin yanzu dai ayyukan ‘yan ta’addan na ci gaba da kawo cikas ga zirga-zirgar al’ummar wannan yanki da ma sauran sassan yankin, lura da cewar gadar na kan hanyar Katarko ne zuwa garin Goneri.

Masu fashin baki kan al’amuran tsaro sun bayyana cewa, lalata wannan gadar mota na iya kawo cikas ga harkokin tsaro a wannan yanki, dalili shi ne yankin na da iyaka da wasu dazuzzukan da su ke da iyaka da dajin Sambisa da ya zama maɓoyar ‘yan ta’addan a wasu ɓangarorin.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button