Jihar Yobe: Gobara ta kona kasuwar Kariyari
Tare da lalata dakarori da kuma dukiyoyin al'umma

Daga Adamu Aliyu Ngulde
Rahotanni daga jihar Yobe a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na cewa gobara ta kona kasuwar Kariyari, da ke karamar hukumar Tarmuwa tare da lalata dakarori da kuma dukiyoyin al’umma.
Wata majiya ta shaidawa Jarida Radio cewa gobarar ta kona shaguna da rumfuna 1,600 sannan mata da dama sun tabka asara ya yin gobarar.
Hakazalika wani ganau ya ce “A yayin da nake magana da kai mahukunta sun kawo ďauki tare da zurfafa bincike domin gano musabbabin gobarar”.
A halin yanzu dai wadanda suka shaida faruwar lamarin sun bayyana irin girman asarar da aka yi, don hakane suke neman tallafin gwamnati da kuma kungiyoyi masu zaman kan su domin ganin sun kawo ďauki ga wadanda iftila’in ya rutsa da su.
Yayin tattaro bayanai game da gobarar, Jarida Radio ta lura da cewa hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Yobe wato (SEMA) ta na tattara bayanan wadanda suka yi asara domin tallafa musu.