‘Yan Boko Haram Sun Kashe ‘Yan Banga Da Masu Aikin Itace a Jihar Borno
'Yan Boko Haram Sun Kashe 'Yan Banga Da Masu Aikin Itace

‘Yan ta’addar Boko Haram sun kashe ‘yan banga 2 da masu sana’ar sayar da itace guda goma a kauyen Bokko Ghide da ke karamar hukumar Gwoza ta jihar Borno.
Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce maharan sun yi wa ‘yan banga (civilian JTF) kwanton bauna tare da kashe su a hanyar Kirawa da ke karkashin gundumar Pulka.
Hare-haren sun zo ne kusan sa’o’i 48 bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da ministan tsaro, Badaru Abubakar, da babban hafsan tsaron kasa, Janar Christopher Musa, da sauran manyan kwamandojin soji domin tantance halin tsaro a jihar Borno.
Ministan tsaro, ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ba da karin tallafin soji domin tunkarar kalubalen tsaro a Borno da arewa maso gabas.