Borno: Sabuwar nakiya ta tashi a wani kauyen Damboa
Wata majiya daga jami'an tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce lamarin ya rutsa da Alhaji Sanda da Bulama Zaraye, wanda ya je daji kona itace domin neman gawayi yayin komawarsa gida ya taka nakiyar.

Daga Adamu Aliyu Ngulde
A rananr Lahadi 6 ga Afrilu wata fashewa da ake kyautata zaton nakiya ce ya jikkata wani mutum a kauyen Masaimari na Karamar Hukumar Damboa da ke jihar Borno, a yankin Arewa Maso Gabashin Nijeriya.
Wata majiya daga jami’an tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce lamarin ya rutsa da Alhaji Sanda da Bulama Zaraye, wanda ya je daji kona itace domin neman gawayi yayin komawarsa gida ya taka nakiyar.
Nakiyar ta raunata shi a hannunsa na dama, cikin gaggawa aka garzaya dashi zuwa asibiti a garin Damboa domin samun kulawar ma’aikatan lafiya.
Har zuwa lokacin rubuta labarin babu wanda ya dauki alhakin harin, sai dai ana zargin mayakan ISWAP ne suka dasa nakiyar kamar yadda suke yi a yankunan da suke da iko musamman a sassan jihar Borno.