Nijeriya

Sojoji sun tarwatsa sansanonin ‘yan bindiga sama da 70 a Taraba

An tarwatsa sansanonin ‘yan bindiga sama da 70 a Taraba

A wani gagarumin yunkuri na kawar da miyagun ‘yan ta’adda a jihar Taraba, dakarun runduna ta 6 na sojojin Nijeriya da kuma sashe na 3 na Operation WHIRL STROKE (OPWS) sun yi nasarar fatattakar wasu ‘yan bindiga tare da tarwatsa maboyarsu da dama a wani samame da suka kai a karamar hukumar Karim Lamido.

Wannan sumame, wanda suka kai a ranar 5 ga Afrilu, wani bangare ne na yakin da ake yi da ‘yan bindiga wanda aka yi wa lakabi da Operation Lafiya Jamaa. An kuma tsara wannan sumame ne domin fatattakar ‘yan fashi da kuma tabbatar da zaman lafiya a sassan jihar Taraba.

A cewar wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Captain Olubodunde Oni, ya fitar, sojojin sun shiga kauyen Achalle,daga nan suka wuce zuwa Chibi, wata matattarar ‘yan bindiga da ta yi kaurin suna.

Sanarwar ta kara da cewa, “Sumamen da aka yi ya kai ga kashe ‘yan bindiga uku. An lalata wasu sansanoni na wucin gadi da ‘yan ta’addan ke amfani da su, sannan sojojin sun kwato babura biyu, da harshashin AK-47 cibiya daya, da harsashi na musamman mai tsawon 7.62mm,” in ji sanarwar.

A yayin da sojojin Najeriya ke ci gaba da kai ruwa rana a karkashin Operation Lafiya Jama’a, sako ga masu ta’addanci a fili yake cewa tabarar da suke yi a Taraba ya zo karshe.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button