Nijeriya

An yanke wa soja hukuncin kisa bisa laifin kisa

Wannan hukuncin ya biyo bayan samun sojan da laifin kashe budurwarsa

Daga Adamu Aliyu Ngulde

Wata kotun soji da ke zamanta a hedikwatar runduna ta 82 ta sojojin Najeriya a Enugu, ta yanke wani soja, Adamu Mohammed hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa laifin kashe budurwarsa mai suna Miss Hauwa Ali.

Kotun sojin da ke karkashin jagorancin shugaban kotun, Birgediya Janar Sadisu Buhari, ta kuma yanke wa wani Abubakar Yusuf hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari bisa samunsa da laifin fashi da makami da ya aikata a wani babban kanti a Enugu.

Mukaddashin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 82, Jonah Unuakhalu, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, an yanke wa masu laifin biyu hukuncin ne bayan kammala shari’ar da ake yi musu na kisan kai da kuma fashi da makami.

Idan za a iya tunawa dai an kafa Kotun Soja mai dauke da mambobi 11, a ranar 18 ga Fabrairu, 2025, ta hannun Babban Kwamandan Runduna ta 82, Oluyemi Olatoye, Manjo-Janar, domin yanke hukunci kan shari’o’in da su ka shafi ma’aikatan rundunar.

Da ya ke bayar da karin haske game da lamarin a yau Talata a Abuja, Unuakhalu, Laftanar-Kanar, ya ce kotu ta yanke hukuncin cewa laifin kisan kai da aka yi wa Mohammed Private yana da hukunci a karkashin sashe na 106 (a) na dokar rundunar soji, Cap A20, dokokin Tarayyar Najeriya, 2004.

Ya kara da cewa, shugaban kotun ya ce an samu sojan da laifin kisan budurwar tasa, inda ya kara da cewa, kwamitin da aka kafa ya gamsu da shaidun da aka bayar a shari’ar.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button