Nijeriya

Borno: Mutum 26 sun halaka a tashin bom

Akalla mutane 26 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu uku suka samu raunuka

Daga Adamu Aliyu Ngulde

Akalla mutane 26 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu uku suka samu raunuka, sakamakon fashewar wani bam a kan hanyar Rann–Kala Balge–Gamboru Ngala a jihar Borno da ke yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Jarida Radio ta gano cewa motocin fararen hula da dama daga Rann a karamar hukumar Kala Balge ne su ka ci karo da wasu bama-bamai da aka binne a hanya.

Hakazalika lamarin ya faru ne a ranar Litinin, bayan da jerin gwanon motocin suka shiga yankin da aka dasa bama-baman cikin dabara.

Sannan motsin motocin ne ya tayar da bama-baman, kuma jami’an agajin gaggawa sun hanzarta zuwa wajen domin kwashe wadanda abin ya shafa da kuma bayar da kulawar gaggawa.

“Dakarun tsaro sun killace hanyar da lamarin ya faru, kuma sun fara gudanar da bincike domin tabbatar da tsaro da kuma hana faruwar irin hakan a nan gaba,” inji wani ganau.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button