Borno: Sabon bam ya sake lakume rayuka da dama a Borno

Daga : Adamu Aliyu Ngulde
A kalla mutum bakwai ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata sanadiyyar fashewar nakiya a hanyar Maiduguri zuwa Damboa da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Jarida Radio ta gano cewa lamarin ya faru da misalin karfe 10:43am na safiyar ranar Asabar ya yin da matafiyar suke hanyar zuwa Maiduguri da ga karamar hukumar Damboa .
Ana kyautata zaton cewa mayakan kungiyar ISWAP ne suka dasa bam din wanda ya lakume rayukan wadanda ba su ji basu gani ba.
Hanyar Maiduguri zuwa Damboa mai nisan kilimita 87 ya kasance shi ne hanya daya tilo da ya hade sauran hanyoyin kudancin Borno daga birnin Maiduguri wanda ake yi wa lakabi da tarkon mutuwa.
A halin yanzu dai tuni aka kwashi wadanda suka jikkata zuwa asbitin kwararru da ke birnin Maiduguri domin samun kulawar likitoci.