Nijeriya

‘Yansandan Kaduna sun zargi El-Rufai da shirya taron siyasa ba bisa ƙa’ida ba

El-Rufai ya shirya taron siyasa ba bisa ƙa'ida ba

Rundunar ‘yansandan Najeriya reshen jihar Kaduna ta zargi tsohon Gwamna Nasir El-Rufai da shirya taron siyasa ba bisa ƙa’ida ba, inda ta ce an yi rikici har da harba bindiga.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, SP Mansir Hassan, ya fitar ta ce ta ƙaddamar da bincike kan rikicin da ‘yandabar siyasa suka yi a garin na Kaduna.

“Binciken farko-farko ya nuna cewa taron ya jawo hatsaniya, inda har ‘yandaba da ‘yan jagaliyar siyasa suka gwabza wanda kuma ya jawo jami’an tsaron da ke tare da tsohon gwamnan suka yi harbin da ya jawo tayar da hankali a jihar,” in ji sanarwar.

Sai dai matasan jam’iyyar haɗaka ta ADC sun yi Allah wadai da rikicin, inda suka zargi jam’iyyar APC mai mulkin jihar da “tura musu ‘yandaba domin hana su gudanar da taron”.

A cewar rundunar ‘yansandan: “Domin gano gaskiyar lamari, mun bincika kuma shugabannin jam’iyyar sun nesanta kansu daga taron, kuma suka musanta iƙirarin tsohon gwamnan da waɗanda suka shirya taron.”

Nasir El-Rufai na cikin jagororin siyasar Najeriya na ɓangaren adawa da suka dunƙule a jam’iyyar haɗaka ta ADC domin ƙalubalantar APC a babban zaɓe na 2027.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button