
Daga Adamu Aliyu Ngulde
A wani labari mai firgici da kuma tada hankali na cewa gobara ta kona sansanin ‘Water Board’ da ke karamar hukumar Monguno a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a ranar 19 ga wannan wata na Afirilu, sannan an yi asarar gidajen tantuna akalla guda ďari.
Shaidun gani da ido sun shaida cewa gobarar ta fara ne daga karfe 10:40 na safiyar ranar Lahadi kafin daga bisani wutar ta karade dukkannin sassan sansanin.
Cikin abubuwan da aka yi asara a sansanin sun hada da; kayan abinci, makwanci da sauran kadarorin ýan gidin hijirar.
Har zuwa lokacin tattaro bayanai ba a gano musabbabin tashin gobarar ba. Hakazalika ana ci gaba da kiyasta girman asarar da aka yi sanadin gobarar.
Tuni dai jami’an bada agaji suka kai ďauki zuwa sansanin domin shawo kan gobarar da kuma kaucewa masu kwasar ganima, sannan jami’an kwana-kwana tare da mazauna sansanin sun yi nasarar kashe gobarar.
Har ila yau babu jikkata ko rasa rai a ya yin gobarar.