Nijeriya
Gwamnatin Adamawa ta sanar da shirin jinya kyauta ga masu ciwon koda
Gwamnan Adamawa Fintiri ya sanar da shirin jinya kyauta ga masu ciwon koda

Daga Mubarak Aliyu
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru a ranar Asabar ya sanar da shirin yin jinyar koda a kyauta a fadin jihar domin sauƙaƙawa ga marasa galihu da ke zuwa a Asibitin Kwararru da ke a nan birnin Yola.
Rahotonni sun bayyana cewa matsakaicin kudin jinyar koda ga mai fama da cutar a kowane mako zai iya kaiwa kimanin Naira dubu 100.
A baya, marasa lafiya da ke fama da cutar koda suna dogaro ne da Asibitin koyarwa na jami’ar Modibbo Adama da ke nan Yola, ko kuma su yi tafiya mai nisa don samun magani a makwabtan jihohi.