
Gwamnatin Jigawa ta amince da ware Naira biliyan 15.8 don gudanar da ingantaccen tsarin ilimi don bunkasa samar da ilimi mai inganci kyauta a jihar.
Kwamishinan Yada Labarai, Hon. Sagir Musa ne ya bayyana haka a ranar Laraba a Dutse.
Ya ce majalisar zartaswa ta jiha ta amince tare da fitar da kudin domin a gaggauta aiwatar da shirin na Jigawa Unified New Improvement of Teaching and Education (Jigawa UNITE).
Hon. Sagir Musa ya ce, an tsara shirin ne don karfafa tura sabbin fasahohin zamani ta hanyar samar da bayanai don samar da ingantattun kayan koyo a shekarar karatu na 2024 zuwa 2026.